25 Yuli 2021 - 17:17
​Najeriya:Hukumar Kula Da Hatsurra Ta Karyata Labarin Faduwar Jirgin Sama A Ilorin Jihar Kwara

Hukumar AIB mai kula da hatsuran jiragen sama ta tarayyar Najeriya ta musanta labaran da suke yaduwa a kafafen sadarwa na yanar gizo, kan cewa wani jirgin sana na kamfanin Peace Air ya yi hatsari a birnin Ilorin na Jihar kwara.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran NAN ya nakalto Mr Tunji Oketumbi shugaban hukumar ta ‘The Accident Investigation Bureau’ AIB, ya na karyata labarin, ya kuma kara da cewa, abinda ya faru shi ne, tayoyin jirgin Peace Air wanda ya sauka a birnin Ilorin ne sun yi bindiga bayan jirgin ya sauka a tashar a ranar 23 ga watan Yulin da muke ciki da misalin karfe 10.30 na safe.

Mr Oketunbi ya kara da cewa al-amarin ya faru ne da jirgin Peace Air mai lamba B737-500 kuma ba bu wanda ya ji ko kwarzane daga cikin fasinjoji 66 da suke cikin jirgen. Sai dai an rufe tashar jiragen sama na Ilorin zuwa wani lokaci don a kauda jirgin daga babban titin saukan jiragen sama. Amma daga baya kome ya koma kamar yadda aka saba.

342/